Scholz yace yakin na bukatar daukar kwararan matakai na tallafa wa Ukraine a kokarin da ta ke yi na kare 'yancin kasarta.
"duk alhakin wannan yakin ya rataya a wuya shugaban Rasha. Shi ya haddasa wannan mummunan al'amari, yakin da ba za a lamunta da shi ba."
A waje guda kuma shugaban gwamnatin na Jamus Olaf Scholz ya bada shawarar gina bututun mai daga Portugal ya ratsa ta Spain da Faransa zuwa tsakiyar Turai domin kawar dogaron kasashen Turai akan makamashin Gas na Rasha.
Yace ya tattauna batun da shugabannin Spain da Faransa da kuma hukumar tarayyar Turai a Brussel.