Olaf Scholz ya isa Jamhuriyar Nijar inda ya fara ganawa da sojojin Jamus da ke aikin horas da dakarun Nijar dabarun yaki da 'yan ta'adda a yankin Sahel.
Yanzu haka kuma shugaban na can yana ganawa da takwaransa na Nijar din Mohammed Bazoum a fadar mulki da ke birnin Yamai, inda tattaunawa tasu ta fi mayar da hankali kan siyasa da ma tsoro a yanklin na Sahel da ke fama da ayyukan 'yan ta'adda.
Wani batu har wa yau da shugabannin biyu za su mayar da hankali a kai shi ne batun bakin haure da ke kwarara zuwa nahiyar Turai ta barauniyar hanya.
Gabannin zuwansa Nijar dai, Scholz ya ziyarci kasar Senegal inda ya tattauna da shugaban kasar Macky Sall kan batutuwan da suka shafi tsaro a Afirka da kuma yakin da Rasha ke yi a kasar Ukraine.