A birnin Berlin da ke zama fadar gwamnatin Jamus, mutane da dama sun yi jerin gwano a wuraren tunawa da tarihi, sai dai kuma an jibge jami'an 'yan sandan don kaucewa barkewar rikici saboda mamayar da Rasha ta kaddamar a Ukraine.
A lokacin da yake jawabi a birnin Berlin, shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce wannan rana ta dade da kasancewa ranar da ake da babban fata sai dai ta bana bata zo da hakan ba, ya na mai alakanta ta da yakin da ke tsakanin Rasha da Ukraine.
Ana nashi jawabin ga 'yan kasa, shugaba gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya kara jadadda goyon bayansa ga Ukraine, ya na mai nuna yakinin cewa Putin ba zai samu nasara a yakin ba.