Wani bincike da gidauniyar nan ta Bertelsmann da ke nan Jamus ta gudanar, ya nuna cewa daga nan zuwa shekarar 2040, kasar na bukatar shigowar ma'aikata baki 'yan kasashen waje dubu dari biyu da tamanin da takwas a duk shekara don yin aiki.
Karin bayani:Scholz ya ce Jamus na bukatar 'yan cirani
Wata babbar jami'ar gidauniyar kuma kwararriya a kan harkokin bakin haure mai suna Susanne Schultz, ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus DPA cewa wajibi ne hukumomin kasar su janye duk wasu tsauraran matakan shigowa Jamus, don bai wa baki damar shigowa domin cike gibin da ake da shi na karancin ma'aikata.