Jamus na bincike kan mutuwar kifaye

Jamus na bincike kan mutuwar kifaye
Kifaye da dama sun mutu a kogin Oder da ke ratsa kasashen Jamus da Poland, lamarin da ya haifar da gargadin bala'in muhalli yayin da aka bukaci mazauna yankin da su kaurace wa ruwan.

Matattun kifayen da ke shawagi a saman ruwa a garin Schwedt da ke gabashin Jamus, ana kyautata zaton sun kwaroro ne daga magudanar ruwan Poland inda aka samu rahotannin farko na mutuwar kifaye da yawa tun ranar 28 ga watan Yuli.

Tuni dai Jamus ta fara bincike don gano sinadarin da ka iya haddasa mutuwar kifayen, rahotannin farko sun nuna alamun yawan ruwan sinadarin dalma. Sai dai wani kashi na sakamakon farko da aka fitar a yammacin ranar Juma'a ya nuna yawan gishirin da ba a saba gani ba.


News Source:   DW (dw.com)