Jamus: Mutum 3 sun kamu da kyandar birrai

Jamus: Mutum 3 sun kamu da kyandar birrai
Masana sun sanar da yadda aka samu karin mutane biyu da suka kamu da kyandar biri a yayin da aka soma baiyana fargabar cutar ka iya zama wata annoba a duniya.

A wannan Asabar aka gano mutane biyu dauke da cutar da aka fi sani da monkeypox a Berlin babban birnin kasar Jamus, akwai fargabar karuwar alkaluman nan gaba in ji sanarwar masana a fannin kiwon lafiya. Wannan na zuwa ne kwana guda, bayan gano mutumin da ake ganin shi ne na farko da ya kamu da cutar a garin Munich da ke Jamus.

Ministan Ma'ikatar Lafiya na Jamus Karl Lauterbach ya ce, an gano yadda za a hana cutar daga yaduwa kuma da wuya ta yadu a cikin jama'a muddun aka dauki matakin na gaggawa. Kawo yanzu, abin da aka sani a game da kyandar biri, asalinta na daga birai amma an fi kamuwa da ita a sakamakon jima'i a tsakanin masu jinsi daya. 


News Source:   DW (dw.com)