Jamus: Matashi ya harbe wata mata a makaranta

Jamus: Matashi ya harbe wata mata a makaranta
'Yan sandan na gduanar da bincike kan maharin da ya illata wata mata lokacin da ya bude wuta a makarantar sakandare a birnin Bremerhaven da ke jihar Bremen. Tuni 'yan sandan suka kama shi.

Dan bindigar mai shekaru 21 da haihuwa, ya bude wuta a wata makarantar sakandare da ke arewacin Jamus, inda ya yi wa wata mata mummunar rauni kafin ya shiga hannun 'yan sanda. 

A wani lamari na daban, 'yan sanda a birnin Leipzig da ke gabashin Jamus sun tsare wani dan makarantar sakadare mai shekara 21 bayan wallafa hotunansa da bindiga a shafin Snapchat tare da yin barazana. Sai dai 'yan sanda sun ce bincike ya gano bindigar ta roba ce kuma bidiyon da ya wallafa wani bangare ne na aikin makaranta.

A makon da ya gabata, masu bincike a birnin Essen sun dakile harin bam a makaranta, bayan sun kama wani matashi dan shekaru 16 da ake zargin yana shirin kai harin ta'addanci na 'yan Nazi. A watan Janairun 2022, wani dalibi dan shekara 18 ya bude wuta a wani dakin karatu na jami'ar Heidelberg da ke Kudu maso yammacin Jamus, inda ya kashe wata budurwa tare da raunata wasu uku.

A shekara ta 2009, wani tsohon dalibin wata makaranta ya kashe dalibai tara da malamai uku a Winnenden da ke jihar Baden-Wuerttemberg ta Jamus. Dan bindigan ya kashe kansa.

A shekara ta 2002, wani tsohon dalibi dan shekara 19 ya harbe mutane 16 a wata makaranta da ke birnin Erfurt da ke tsakiyar Jamus, shi ma ya kashe kansa. Wannan hare-hare dai sun sa gwamnatin Jamus tsaurara dokokin mallakar bindiga na neman tilasta 'yan kasa da shekaru 25 su yi gwajin lafiyar kwakwalwa kamin neman lasisin mallakar bindiga.


News Source:   DW (dw.com)