Sakamakon farko na kuri'un da aka kada a zaben 'yan majlisun jihar North Rhine-Westphalia da ke Jamus, na nuni da cewar jam'iyyar shugaban gwamnati Olaf Scholz ta sami mumunan koma baya a wannan zaben da ke zama zakaran gwajin dafi ga sabuwar gwamnatin da ta dare karagar mulki a shekarar da ta gabata.
Jam'iyyar CDU wacce ta yi nasara a zaben ta sami kaso 35 cikin dari. Ita kuwa jam'iyya mai mulki ta SPD ta sami kaso 28 ne kacal cikin dari, inda ta yi kasa da sama da kaso 3 a zaben na jihohi da ya gudana.
Da wannan sakamako hakan na nuni da cewar gamayyar kawancen gwamnati da ke tsakanin jam'iyyun CDU da FDP, yanzu haka ba za su sami rinjaye a majalisar ba abin da ke nuni da cewa tilas a sake zama kan teburin tattauna yiwuwar sake kafa gwamnatin hadaka a jihar.