Goyon bayan jama'a ga kawancen jam'iyyun CDU da CSU masu matsakaicin ra'ayin rikau ya ragu da kimanin kashi biyu zuwa kashi 28 cikin dari gabanin zaben da ake shirin gudanarwa a ranar 23 ga wannan watan na Fabrairu kamar yadda kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka fitar ta nuna.
Raguwar goyon bayan dai ya samu ne bayan da dan takarar neman mukamin shugaban gwamnati a karkashin inuwar jam'iyyar CDU Friedrich Merz ya hada kai da Jam'iyyar AfD mai akidar kyamar baki wajen zartar wani kudiri da ke da manufar datse iyakokin kasar ga 'yan cirani. Wannan kaucewa akida ne da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin Jam'iyyar.
Sakamakon da Jam'iyyar ta samu na kuri'ar jin ra'ayin jama'a shi ne mafi kankanta tun bayan wanda aka yi a watan Oktoban 2023 kan Jam'iyyar ta CDU wadda tsawon watanni ke kan gaba.
Kuri'ar wadda cibiyar nazari ta Forsa ta gudanar ta nuna Jam'iyyar AfD mai kyamar baki ba ta sauya ba, tana nan a matsayi na biyu da kashi 20 cikin dari.
Jam'iyyar Social Demokrats ta shugaban gwamnati Olaf Scholz tana da kashi 16 cikin dari yayin da the Greens mai rajin kare muhalli ta ke da kashi 15 cikin dari.