Rahotannin sun nunar da cewa jadawalin kasuwanci a Jamus ya sauka daga kusan sama da kaso 92 cikin 100 a watan Yunin da ya gabata, zuwa sama da kaso 88 a wannan wata na Yuli da muke ciki. Wanin bincike ya nunar da cewa farashin makamashi ya yi tashin gauron zabi, kana barazanar karancin iskar gas na kara sanya fargaba. Jadawalin kasuwanci na ifo a Jamus, ya yi gargadin cewa kasar ka iya fadawa cikin masassarar tattalin arziki. Wannan matsala dai ta biyo bayan kokarin farfadowa da tattalin arzikin ke yi daga matsalar sama da shekara guda, wato tun daga farkon shekara ta 2020 sakamakon bullar annobar corona.