Tuni shugaban gwamnatin na Jamus ya isa birnin New Delhi tare da rakiyar manyan ministocin gwamnatinsa domin tattaunawar da kasashen biyu suka dabbaka a shekarar 2011.
Karin bayani: Ziyarar shugabar gwamnatin Jamus a ƙasar India
Gabanin taron na birnin New Delhi shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce kasarsa na bukatar kawaye irin su Indiya wajen karfafa alakar kasuwanci da kuma tsaro, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.
Karin bayani:Yaki ka iya mamaye Gabas ta Tsakiya - Scholz
Wannan ita ce ziyara ta uku da Scholz ya kai Indiya tun bayan da ya hau kan karagar mulki a shekarar 2021. Kazalika shugaba Scholz ya ziyarci kasar Indiya sau biyu a shekara ta 2023, a yayin da ya halarci taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20.