Jamus: An kama wasu mutane 4 da ke shirin lalata wutar lantarki

Jamus: An kama wasu mutane 4 da ke shirin lalata wutar lantarki
An kama wasu Jamusawa 4 da shirinn kaddamar da wasu ayyukan ta'addanci da ma kokarin sace wasu manyan jami'an gwamnati.

Jami'an tsaron kasar Jamus sun yi nasarar damke wasu mutane 4 da ake zarginsu da zama masu tsatsauran ra'ayi a kan maufofin gwamnati wadanda kuma ke da shirin lalata hanyar samar da makamashin lantarki a kasar da ma shirin sace wasu kusoshin gwamnati ciki harda ministan lafiya.

A cewar ministar harkokin cikin gida Nancy Faeser daga binciken da aka gudanar an gano mutanen sun jima suna kitsa yadda za su lalata hanyar wutar lantaki da za a jima ana zama cikin duhu, da ma munanan yunkurin ayyukan ta'addanci.

An kaddamar da sumame ne a gidaje sama da 20 a fadin kasar inda aka yi nasarar kama manya da kananan makamai. 

Masu shigar da kara da ke birnin Koblenz na jihar Rhineland- Palatine sun ce mutanen da aka kama na daga cikin wadanda suka yi ta shirya zanga-zangar kin jinin matakan gwamnati a kan yaki da cutar corona. Yanzu haka mutane 12 ne aka bincike a kansu.


News Source:   DW (dw.com)