Jam'iyyun siyasar Jamus na karkare yakin neman zaben Lahadi

A wannan Asabar jam'iyyun siyasar Jamus ke karkare yakin neman zabe da ke zama jajiberin babban zaben ranar Lahadi, inda gamayyar jam'iyyun CDU-CSU ta shriya gudanar da gangami a birnin Munich na jihar Bavaria cikin tsauraran matakan tsaro.

Karin bayani:Sabbin manufofin ketare na taka rawa a zaben Jamus

Masu gabatar da jawabai a taron za su mayar da hankali kan hadin kan jam'iyyun don ganin sun samu nasarar lashe zabe, tare da kafa gwamnati, wadda ka iya fuskantar kalubale ga sabon shugaban gwamnatin.

Karin bayani:Muhawara mai zafi gabanin zaben Jamus

Friedrich Merz na CDU da ke kan gaba a cikin 'yan takarar, na daga cikin masu gabatar da jawabi, sai jagoran CSU Markus Söder, da kuma 'dan takararsu Alexander Dobrindt.


News Source:   DW (dw.com)