Sanarwar hukumar ta bayyana cewa jam'iyyar shugaba Mahamat Idriss Deby ta Patriotic Salvation Movement, ta samu kujeru 124 daga cikin 188 a majalisar dokokin kasar, yayinda sauran jam'iyyun hamayya da suka shiga zaben suka samu kujeru 30.
Karin bayani: An kai hari fadar shugaban kasar Chadi
Jam'iyyar jagoran adawar kasar Success Masra ta "The Transformers" ta kauracewa shiga zaben, sakamakon zargin tafka magudi da kuma rashin sakarwa 'yan adawa mara wajen shiga al'amuran da suka shafi siyasar kasar ta Chadi.
Karin bayani: 'Yan adawa sun kaurace wa tagwayen zabukan Chadi
Deby ya hau kan karagar mulkin kasar a 2021, bayan 'yan ta'adda sun halaka mahaifinsa Idriss Deby a fagen daga.