Wani hasashe da gidan talabijin din gwamnatin Japan na NHK ya fitar na nuni da cewa jam'iyya mai mulki ta firaminista Shigeru Ishiba ta barar da rinjiyenta a majalisar dokokin kasar a zaben 'yan majalisu da aka gudanar a wannan Lahadi. Idan ta tabbata wannan shine karon farko tun shekarar 2009 da jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya ta LDP da ta dade tana jan zarenta a fengen siyar Japan ke rasa jinjaye a majalisa.
Karin bayani: Firaministan Japan ya tsallake rijiya da baya
Sai dai har kawo wannan lokaci, hasashen da aka bayar a bisa la'akari da sakamakon da ya fito daga akwatinan zabe bai kai ga hakikance cewa ko kawancen LDP da abokiyar tafiyarta Komeito ya samu gagarumin rinjayen da zai ba shi damar kafa gwamnati ba. Hasashen dai ya yi nuni da cewa kawancen ja'iyyun na iya lashe kujeru 174 zuwa 254 daga cikin kujeru 465 na majalisar inda ake bukatar adadin kujeru 233 domin samun rinjaye.