Manyan jami'an diflomasiyyar Amurka da na Rasha za su gana da juna a birnin Riyadh na kasar Saudi Arebiya ranar Talata, don warware tsamin dangantakar ke tsakaninsu, tare da lalubo hanyoyin kawo karshen yakin Ukraine da Rasha.
Bangarorin biyu na da ra'ayin cewa ba lallai ne ganawar wadda ita ta farko ta kawo karshen yakin ba, tun bayan da Rasha ta fara kai wa Ukraine hari a cikin shekarar 2022.
Karin bayani:Ukraine: Putin na neman hanyar juya gwamnatin Trump
Tuni dai Ukraine da kuma kasashen Turai suka shiga tababar me ka je ya zo game da wannan tattauna ta musamman da shugaban Amurka Donald Trump ya shirya ba tare da tuntubarsu ba, inda su ma suka tsara wani taro a Paris babban birnin Faransa a Litinin, don sanin irin martanin da za su mayar a kai.
karin bayani:Hungary ta zargi Turai da yin kafar ungulu a yakin Ukraine
Mai magana da yawun fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce taron zai fara mayar da hankali ne kan yaukaka alaka tsakanin Amurka da Rasha, sannan su dora da batun Ukraine, ciki har da ganawar keke-da-keke tsakanin shugaba Trump da takwaransa Putin.