Tun bayan sake bullar kungiyar M23 da ke samun goyon bayan Kigali a shekarar 2021, sun kwace iko da yankunan Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango, tare da raba dubban mutane da dama da matsugunnansu. Ko a watan Augusta, kasar Angola ta shiga tsakani a rikicin Kwango na Ruwanda, inda aka cimma wata kwarya-kwaryar yarjejeniya daidaita al'amura fagen daga, sai dai bangarorin biyun sun cigaba da musayar wuta yayin da kazamin fada ya sake barke wa a watan Oktoba.
Karin bayani: Zaman lafiya a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Shugaban Angola, Joao Lourenco da kungiyar Tarayyar Afirka ta nada a matsayin mai shiga tsakani na fatan cewa ganawar ta Luanda, za ta kai su ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya. A yanzu dai, 'yan tawayen M23 da kuma dakarun Ruwanda sun kusa mamaye arewacin Kivu, na lardin Goma mai yawan al'umma kimanin miliyan daya yayin wasu miliyan daya suka rasa matsugunnansu sakamakon rikicin.