Somaliland dai na cin gashin kanta tun bayan ballewa daga kasar Somaliya a 1991, duk da cewa hukumomin kasa da kasa basu amince da ita ba a matsayin kasa mai cikakken iko wanda hakan ya sanya hukumomin kakaba mata takunkumin karayar tattalin arziki da kuma hana manyan jami'an gwamnatin yankin zirga-zirga a kasashen ketare.
Karin bayani: An gudanar da zaben shugaban kasa a Somaliland
Hukumar zaben kasar ta ce jagoran adawar Mr. Irro na jam'iyyar Waddani ya lashe zaben da kaso 64% bisa 100, yayin da shugaba mai ci Bihi ya samu kashi 35% bisa 100 na yawan kuri'un da aka kada.
Ana sa ran rantsar da sabon shugaban a ranar 14 ga watan Disambar 2024. Irro ya taba zama jakadan Somaliya a tsohuwar Tarayyar Soviet da kuma Finland, kazalika ya kuma taba zama kakakin majalisar dokokin Somaliya mafi dadewa kafin ballewa daga kasar.