Ja-in-ja tsakanin soji da farar hula a Guinea

Ja-in-ja tsakanin soji da farar hula a Guinea
Gwanmnatin mulkin soji a Guinea Conakry ta rusa wata kungiyar ta kawancen 'yan siyasa da kuniyoyin farar hula da na kwadogo da ke adawa da gwamnatin.

Kungiyar wacce ta jagoranci zanga-zangar adawa da tsohon shugaban ƙasar Alpha Condé bayan da ya yi tazarce. Ta sake bujerawa sojojin watannin kadan bayan juyin mulkin da suka yi kan hujjar cewar  ba su da niyyar mika mulki ga farar hula. A cikin wata sanarwa da ta bayyana gwamnatin ta ce kungiyar na yin barazana ga zaman lafiya da hadin kan kasa a Guinea don haka ya zama wajibi da a soketa. Sojojin da ke rike da madafun ikon Guinea sun yi alkawarin mika mulki ga farar hula a cikin shekaru uku sai dai kungiyar ta ki amincewa da haka.

 


News Source:   DW (dw.com)