Ivory Coast ta koma amfani da burodin rogo

Ivory Coast ta koma amfani da burodin rogo
Ivory Coast ta dauki matakin maye gurbin alkama da rogo don sarrafa burodi saboda tsadar alkaman a sakamakon yakin Rasha da Ukraine.

A yayin da farashin alkama ke kara hauhawa a kasuwannin duniya a sakamakon yakin gabashin Turai, kasar Ivory Coast da ke yankin yammacin Afirka ta koma amfani da rogon da ta ke nomawa a cikin kasar wajen yin burodi, akasarin 'yan kasar na dogaro da burodi don karin kummalo, lamarin da ya jefa jama'a da dama cikin mawuyacin hali, amma yanzu gwamnatin ta soma tallafa wa masu gidajen burodin, inda ta nemi su dinga surka alkaman da rogon na cikin gida wajen yin burodin don wadata jama'a.

Ivory Coast na noma sama da tan miliyan shida na rogo a duk shekara kuma tuni 'yan kasa da dama suka goyi bayan shirin gwamnatin da ake ganin zai taimaka wajen habbaka tattalin arzikin kasar. A bara kadai, kashi 10 cikin 100 na kasafin kudin kasar na kusan dala biliyan 16, an kashe su ne wajen shigo da abinci daga kasashen waje amma yanzu dole gwamnati ta dauki mataki ganin yadda kasashen duniya da dama ke fama da tsadar kayayyakin abinci.
 


News Source:   DW (dw.com)