ISWAP ta kashe mutane a Chibok

'Yan bindigar kungiyar ISWAP, sun kai wani sabon hari a kauyen Chibok da ke arewacin Najeriya inda suka kashe mutane da kona gidaje da ma kwashe kayan abinci da farfasa shaguna.

Rahotannin da ke fitowa daga yankin arewa maso gabashin Najeriya, sun tabbatar da wani sabon hari da mayakan tarzomar ISWAP suka kai wani kauyen Chibok da ke cikin jihar Borno.

Bayanai sun ce akalla mutum tara ne suka salwanta a harin da aka kai kauyen Kautikeri da yammacin jiya Talata, daidai lokacin da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ke ziyara a jihar.

Shaidu sun ce maharan da suka shiga cikin motoci wasu bisa babura, sun kuma kwashe kayan abinci da na shaguna a suka samu a kauyen.

Sojojin Najeriya dai ba su bayar da tabbacin faruwar harin a lokacin da ya faru ba, sai dai dagacin kauyen, Ayuba Alamson ya tabbatar da faruwar lamarin.


News Source:   DW (dw.com)