Wata majiya ta kusa da mayakan Hezbollah na Lebanon ta ce hare-haren da dakarun Isra'ila suka a kudancin birnin Beirut fadar gwamnatin kasar sun ritsa da daya daga cikin wuraren da kungiyar take gudanar da ayyukanta. Daruruwan farmaki dakarun Isra'ila suka kaddamar a yankunan kudanci da gabashin Lebanon a wannan Litinin.
Fiye da mutane 270 suka halaka sakamakon hare-haren na dakadun Isra'ila yayin da wasu darauruwa suka jikata.
Tuni Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya yi gargadi kan abin da 'yan Hezbollah za su fuskanta daga dakarun kasarsa. Firaministan ya bayyana cewa mayakan Hezbollah za su fuskanci sakamakon jefa rayuwar 'yan Isra'ila cikin kasada da suka yi.