Majalisar tsaron Isra'ila ta amince da yarjejeniyar da gwamnati ta cimma da kungiyar Hamas a kan Zirin Gaza, wacce ke share fagen fara tsagaita wuta a ranar Lahadi da kuma sako wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su. Ita ma majalisar ministoci na taro don daukar matakin karshe, duk da adawar da ministocin da ke da ra'ayin rikau ke nunawa. Sai dai, sojojin Isra'ila suna ci gaba da kai hare-hare ta sama kan yankin Falasdinawa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dari cikin kwanaki biyu, a cewar masu aikin ceto.
Karin bayani: Martani kan tsagaita wuta a yakin Gaza
Hukumomin Isra'ila sun sanar da daukar matakan rigakafi don kauce wa abin da ka iya zuwa ya dawo a yayin nuna farin ciki a lokacin da za a musayar fursunoni. A yunkurin aiwatar da matakin farko na yarjejeniyar dai, Hamas ta yi alkwarin sakin mutane 33 da ta yi garkuwa da su ciki har da mata uku, yayin da Isra'ila za ta sako Falasdinawan da take tsare da su a gidajen yarinta.