Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce, Yahya Sinwar na daga cikin 'ya ta'adda uku da dakarun kasar suka kashe a farmakin da suka kai Zirin Gaza. Isra'ila dai na zargin Sinwar da kitsa kai mata hari mafi muni a tarihinta a ranar bakwai ga watan Octoban shekarar bara.
Sanarwar da Isra'ila dai na zuwa ne makwanni bayan da ta kashe shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah a wani mummunan harin da ta kai Lebanon.
Karin bayani: An yi jana'izar shugaban Hamas a Iran
Sinwar dai ya zama shugaban Hamas ne bayan da aka kashe tsohon shugaban kungiyar, Ismail Haniyeh a watan Yulin da ya gabata, kana yana daga cikin wadanda Isra'ila ke nema ruwa a jallo.