Isra'ila ta kashe babban kwamandan Hamas na Lebanon

Kungiyar Hamas ta Falasdinawa da ke yaki da Isra'ila a Gaza, ta ce hare-haren Isra'ila a kudancin Lebanon sun halaka babban kwamnadanta na Lebanon din Fateh Sherif Abu el-Amin, tare da wasu iyalansa.

Karin bayani:Fargabar ta'azzarar rikici bayan kisan Nasrallah

Baya ga kwamandan na Hamas da hare-haren na dakarun Isra'ila na jirage marasa matuka na Litinin din nan suka halaka, akwai wasu kwamandoji uku wato Mohammad Abdel-Aal, da Imad Odeh da kuma Abdelrahman Abdel-Aal.

Rundunar sojin Isra'ila ta sha alwashin ci gaba da kai farmaki Lebanon, har sai ta murkushe duk wani burbushi na kungiayr Hezbullah da aminiyarta Hamas ta Falasdinu, wadanda ke samun goyon bayan Iran.

Karin bayani:Yaki ka iya mamaye Gabas ta Tsakiya - Scholz

A daren Lahadi ne ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot, ya gana da firaministan Lebanon Najib Mikati a Beirut babban birnin kasar, inda ya yi kira ga Isra'ila da ta dakatar da barin wuta a Lebanon nan take.


News Source:   DW (dw.com)