Isra'ila ta kashe akalla mutum 22 a zirin Gaza cikinsu har da yara biyar a cewar jami'an kiwon lafiyar Falasdinawa.
Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da wasu Kiristoci a zirin suka fara gudanar da addu'o'in Kirsimetin 2024.
A wani harin na daban, sojojin na Isra'ila sun far wa jama'a tare da kashe mutum biyu a cikin wata mota a kudancin garin al-Mawasi da kuma wani harin a arewacin Gaza.
Isra'ila ta kai jerin farmaki a Yamen
Kusan Falasdinawa miliyan biyu ne ke neman kare kansu daga sanyi a yayin da Isra'ila ke ci gaba da kaddamar da hare-hare a zirin.
Isra'ila ta aikata 'kisan kare dangi' a Gaza - Amnesty International
Farashin barguna da itace da kuma tufafi ya yi tashin gwauron zabi saboda yanayin sanyi da ake fama da shi.