Isra'ila ta kama wanda ya harbe mutane a bas

Isra'ila ta kama wanda ya harbe mutane a bas
Wani dan bindiga ya bude wuta kan wata motar safa a kusa da tsohon birnin Kudus, inda ya raunata akalla ‘yan Isra’ila bakwai. Biyu daga cikin wadanda abin ya shafa na cikin mawuyacin hali.

'Yan sandan Isra'ila  sun kama mutumnin da ya bude wuta kan wata motar bas a kusa da wurin ibadar Yahudawa a ranar Asabar, inda ya jikkata akalla mutane bakwai.

"An kawo mutane 6 da suka ji rauni a sashinmu, biyu na cikin mummunan yanayi - akwai mace mai ciki da ta ji rauni haryanzu tana dakin tiyawa. da wani mutum mai shekaru 60 da ya samu rauni a wuyansa da kai, wasu mutane hudu na fama da rauni a kirji da gabobin jikinsu." inji wani daraktan rukunin taimakon gaggawa a cibiyar kiwon lafiya ta Shaare Zedek.

Harin dai na zuwa ne mako guda bayan kazamin fada na tsawon kwanaki uku tsakanin Isra'ila da 'yan faftukar jihadi a yankin zirin Gaza, an kiyasta mutuwar mutane 49, kasar Masar ce ta jagoranci shiga sulhu don samun zaman lafiya.


News Source:   DW (dw.com)