Sojojin Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a tungaye da dama na kungiyar Hezbollah a birnin Beirut da kudancin kasar Lebanon. Sannan suna ci gaba da kai farmaki a kan Hamas a Zirin Gaza, inda wani harin ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 70 a ranar Asabar, a cewar jami'an agajin gaggawa. A yakin da suke yi da wadannan kungiyoyi da Iran ke mara wa baya, sojojin Isra'ila sun sanar da cewa sun kai hare-hare a wurare 175 a yankin Falasdinawa da kasar Lebanon a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, ciki har da ma'ajiyar makamai da wuraren harba rokoki na Hamas da Hezbollah.
Karin bayani:
Hotuna daga Lebanon sun nuna girman barna a Beirut
Isra'ila ta ci gaba da kai farmaki a Lebanon har tsakiyar babban birnin kasar Beirut. A cewar hukumomin Lebanon akalla mutane 2000 suka mutu tun daga makon jiya
Hoto: -/AFPWuta da Barna
Sojojin Isra'ila na ci gaba da kai munanan hare-hare ta sama kan wasu wurare a Lebanon, kamar yadda aka gani a safiyar ranar 3 ga watan Oktoba a Beirut. Sojojin Isra'ila sun ce suna kai farmaki kan wuraren da mayakan Hizbullah masu samun goyon bayan Iran suka boye. Isra'ila ta tura sojojinta na kasa a kudancin Lebanon tun ranar 1 ga Oktoba.
Hoto: Amr Abdallah Dalsh/REUTERSKomai ya ruguje
An dauki wannan hoton ne a safiyar Alhamis, daya daga cikin gundumomin kudancin Beirut. Jiragen yakin Isra'ila sun kai hari a wasu wuraren kudancin Lebanon da kwarin Bekaa da ke da tazarar kilomita 60 daga gabashin babban birnin kasar.
Hoto: Mohamed Azakir/REUTERSHari a tsakiyar birnin Beirut
Wani harin da Isra'ila ta kai wa wani gini a unguwar Bashoura da ke tsakiyar birnin Beirut. A cewar majiyoyin Isra'ila, ginin yana dauke da ofishin hukumar lafiya ta Musulunci, wanda ke da alaka da kungiyar Hizbollah. Haka zalika, ginin yana kusa da ofishin firaministan kasar da majalisar dokokin Lebanon.
Hoto: Emilie Madi/REUTERSFarkawa cikin tashin hankali
Yayin da rana ta fito kan baraguzan hayaki a gundumar Moawwad ta kudancin Beirut a ranar Alhamis, mazauna yankin sun yi nazarin irin barnar da aka yi a unguwarsu.
Hoto: -/AFPNeman mafaka a gidajen rawa
Mutanen da suka yi asarar gidajensu sun yi nasarar samun matsuguni a shahararen gidan rawa na Skybar, an fi sanin wannan gidan da rayuwar dare a Beirut. Mutane sun kasance suna taimakon juna ta hanyar shirya agajin gaggawa da abinci da wurin kwana.
Hoto: Louisa Gouliamaki/REUTERSKwana kan Titi
Dandalin Shahidai mai nisan kilomita daya daga tashar jiragen ruwa a tsakiyar birnin Beirut, shi ma ya zama sansani da mafaka ga iyalai. Da yawa na cikin rudani, sun rasa duk abin da ba za su iya dauka ba, kuma ba su san abin da za su yi ba.
Hoto: Ugur Can/ABACA/abaca/picture allianceTsaftacewa na wucin gadi
Watakila za a dauki lokaci kafin a sake gina gidajen da aka lalata. Rikicin kawo karshe ba, amma a halin yanzu ana share baraguzan tituna ta hanyar amfani da wadannan kananan motocin shara.
Hoto: Mohamed Azakir/REUTERSHotuna 71 | 7Hotuna 7Isra'ila ta ce wannan hafsnta sojanta ya mutu a farmakin, yayin da a nata bangaren, kungiyar Hezbollah ta dauki alhakin hare-haren rokoki da aka kai birnin Haifa, da wani sansanin soji da ke kusa da Safed da ke arewacin Isra'ila, da kuma kan wasu sojojin Isra'ila a kudancin Lebanon.