A baya bayan nan Israila ta tsananta hare hare ta sama a arewa maso gabas da kuma kudancin Lebanon. Masu shiga tsakani na kokari domin samun yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon da kuma Gaza.
Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce mutane fiye da 2,800 suka rasa rayukansu yayin da wasu 13,000 kuma suka sami raunuka tun daga ranar 8 ga watan Oktoba lokacin da Hizbullah ta fara harba rokoki zuwa cikin Israila.
Yawan mutanen da suka rasu a yakin Israila da Hamas a Gaza ya haura mutum 43,000 yayĆn da harin da Hamas ta kai wa Israila na ranar 7 ga wata Oktoba ya hallaka 'yan Israila 1,200 yawancin su fararen hula ta kuma yi garkuwa da wasu mutanen 250