Rundunar sojan Isra'ila ta ce ta kai gagarumin farmakin da jiragen yaki ciki har da jirage marasa matuka da sauran kayan yaki, duk an turasu a yankin kasar Yamen mai nisan kilo mita 1,700 daga Isra'ila. Hare-haren Isra'ilan dai sun ragargaza tashoshin makamashi a Sana'an babban birnin kasar ta Yamen. Wata sanarwar da aka wallafa ta ce Benjamin Netanyahu firimiyan Isra'ila, ya dau wadannan matakai kai hari cikin Yamen ne, a martani kan jerin hare-haren da mayakan Houthi suka yi ta kai wa Isra'ila, inda ko a wannan Alhamis wani harin mayakan Houthi da ya rutsa da wata makaranta a cikin Isra'ila. Tun fara yakin Gaza ne dai mayakan Houthi ke kai hare-hare wa Isra'ila a matsayin gudumawa ga Palastinawan Gaza wadanda Isra'ila ke kai wa farmaki tun bayan harin bakwai ga watan Oktoba.