Isra'ila ta kai hari a iyakar Labanan da Syria

Isra'ila dai ta zargi kungiyar ta Hezbollah da saba yarjejeniyar tsagaita wuta wajen amfani da wannan kafa ta fasa kwaurin makaman daga Syria.

Haka ma sojojin na Isra'ila sun ce suna gudanar da bincike a kudancin Labanan, inda cikin sa'o'in da suka gabata ta gano makamai da aka boye a wani masallaci.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki.

Yana daga cikin abin da yarjejeniyar ta kunsa, sojojin Labanan da na Majalisar Dinkin Duniya za su kasance a kudancin, inda su kuwa daga nasu bangaren sojojin Isra'ila za su janye na tsawon kawanaki 60.

Bangarorin biyu na zargin juna da saba yarjejeniyar.


News Source:   DW (dw.com)