Isra'ila ta kai hare-hare kan kungiyar Hezbullah a Lebanon

Sojojin Isra'ila sun sanar da kai hare-haren bama-bamai a cibiyoyi kusa 100 na Hezbollah a kasar Lebanon, kwanaki biyu bayan da kungiyar ta sha alwashin daukar fansa bayan fashe-fashen wayoyin salular membobinta. Yayin da jagoran Hesbollah wato Hassan Nasrallah ke gabatar da jawabi ne, jiragen Isra'ila suka yi shawagi a birnin Beirut kuma suka kai hare-hare a kudancin Lebanon, domin a cewarsu lalata rumbunan ajiyar rokokin na Hezbollah. Wadannan hare-haren na daga cikin mafi muni tun bayan fara musayar wuta a kan iyakar Isra'ila da Lebanon a watan Oktoban 2023.

Karin bayani: Gaza zai iya ruruta rikicin Isra'ila da Hezbollah

A nata bangaren, kungiyar Hezbollah ta dauki alhakin harba makami mai linzami ga Isra'ila a matsayin ramuwar gayya baya ga  hare-hare akalla 17 da ta kai a ranar Alhamis kan wasu cibiyoyi 14 na soji a arewacin Isra'ila. Sannan kungiyar da ke dauke da makamai tana ci gaba da zargin Isra'ila da kashe membobinta 37 tare da jikkata wasu karin 2,931, lamarin da ta ce sai ta rama. Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya da kasar Amurka suka yi gargadin cewar wadanan hare-hare na iya kara farfado da rikici a yankin Gabas ta Tsakiya, kusan shekara guda bayan fara yaki tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas a Zirin Gaza.

 


News Source:   DW (dw.com)