Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce, Isra'ila ta bayyana wa Majalisar Dinkin Duniya a hukumance cewa ta haramta ayyukan hukumar bayar da agajin Falasdinawa ta Majalisar UNRWA. A watan da ya gabata ne 'yan majalisar dokokin Isra'ila suka bukaci a haramta ayyukan hukumar a Isra'ila, da dakatar da dukannin wani hadin kai da Isra'ila ke bai wa hukumar da ake ganin a matsayin madogara ga miliyoyin Falasdinawa, da ke gabar yamma da kogin Jordan da kuma Zirin Gaza.
Karin bayani: Majalisar dokokin Isra'ila na shirin haramta wa MDD aikin agaji a Falasdinu
Isra'ila dai ta zargi hukumar da rashin adalci da ma hannun wasu daga cikin ma'aikatanta a harin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Octoban shekarar 2023. Ko da yake matakin ya takaita aikin hukumar a gabar yamma da kogin Jordan , sai dai hakan zai yi mummunan tasiri kan aiki jin kai na hukumar, wanda dama ke fuskantar kalubale na karancin kayan agaji a Gaza.