Isra'ila ta fice daga kwamitin kare hakkin bil Adama na MDD

Ministan harkokin wajen Isra'ila Gideon Saar ne ya sanar da hakan, inda ya ce sun yanke hukuncin daukar wannan mataki ne bisa la'akari da nuna banbanci da ake nuna musu tun bayan samar da hukumar a shekarar 2006.

Ministan ya kara da cewar Isra'ila ta yi maraba da matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na kin shiga kwamitin na kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya UNHRC, a cewar sa Isra'ila ta bi sahun Amurka.

 


News Source:   DW (dw.com)