Mazauna yankin da suka nemi a saka sunayensu sun ce wani gini ya rushe sakamakon harin a garin Chiyah da ke kusa da kudancin Beirut, sai dai ba a samu asarar rayuka ba sakamakon tsere wa da mazauna garin suka yi gabanin harin.
Tun da fari, a sakon da ya wallafa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a baya, kakakin rundunar sojin Isra'ila ya ce, Isra'ila za ta fara kai hare-hare kan gine-gine mallakin bankin Al-Qard Al-Hassan, bankin da Amirka ta ce Hezbollah na amfani da shi wajen gudanar da harkokin kudinta.
Bankin na da rassa kimanin guda 30 a Lebonan ciki har da 15 da ke a cikin Beirut da kewaye. Sai dai Kungiyar Hezbollah da gwamnatin Lebanon ba su ce uffan ba kan wannan matakin na Isra'ila.