Kakakin rundunar Isra'ila Rear Admiral Daniel Hagari ya ce harin ya kashe fararen hula da Ibrahim Aqil da ke zama kwamandan rundunar Al-Radwan, wanda Amurka ke nema sakamakon zarginsa da marar hannu a harin Beirut a shekarar 1983. Amma bayan hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai Beirut wanda suka yi kashe kwamandojin Hesbollah, kungiyar ta dauki alhakin harba wa isar'ila rokoki 140 tare da alkawarin daukar fansa.
Krin bayani: Zaman tankiya kan iyakar Lebanon da Isra'ila
Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan halin da ake ciki a Lebanon musamman dangane da hare-haren Isra'ila ke kaiwa, inda ta yi kira ga bangarorin biyu da suka kai zuciya nesa. Ita ma Kungiyar Hamas da ke yaki da Isra'ila a zirin Gaza, ta yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai a birnin Beirut, tana mai danganta kashe daya daga cikin shugabannin Hezbollah na kasar Labanon da mummunan tashin hankali.