Isra'ila ta ce Hezbollah ta kai harin jirgi maras matuki kusa da fadar firaminista Benjamin Netanyahu

Isra'ila ta ce Hezbollah ta kai harin jirgi maras matuki kusa da fadar firaminista Benjamin Netanyahu a wannan Asabar, inda ya fada kan wani gini, to amma fMr Netanyahu da mai dakinsa ba sa cikin gidan lokacin da aka kai harin.

Sanarwar fadar ta ce harin bai raunata kowa ba, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito.

A gefe guda kuma rundunar sojin kasar ta ce an harba ma ta makamai masu linzami 115 daga Lebanon a wannan Asabar, inda jiniyar ankarar da jama'a ta rinka kara a arewacin kasar a lokuta da dama.

Karin bayani:Amurka za ta aika sojojinta Isra'ila

Kasar Turkiyya dai ta ce farmakin da Isra'ila ke kai wa Lebanon da Gaza ka iya fusata Iran har ta dauki matakan da suka dace a kanta.

Ministan harkokin kasar kaar Hakan Fidan ne ya sanar da hakan a birnin Santunbul, yayin taron manema lamarai da ya gudanar tare da takwaransa na Iran Abbas Araghchi, yana mai gargadin cewa wajibi ne a dauki matakin dakile rincabewar rikicin yakin Gabas ta Tsakiya.

Karin bayani:Turkiyya ta lashi takobin hukunta masu hannu a harin Rafah

Iran ta tunzura ne bayan da Isra'ila ta kashe jagororin kungiyar Hamas ta Gaza Isma'il Haniyeh da Yahya Sinwar, da na Hezbollah ta Lebanon Hassan Nasrallah, wadanda Iran ta jima tana marawa baya.

A kokarinta na mayar da martani ne Iran ta kai wa Isra'ila hare-haren makamai masu linzami kusan 200 a ranar 1 ga wannan wata na Oktoba, kuma tun bayan wannan hari ne Isra'ila ta sha alwashin yin ramuwar gayyar da za ta jikkata Iran, amma Iran ta ce idan Isra'ila ta yi hakan to za ta gane kurenta.

 


News Source:   DW (dw.com)