Isra'ila ta bukaci tsawaita yarjejeniya har bayan Ramadan

Ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya amince da bukatar Amurka na tsawaita wa'adin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni har zuwa bayan azumin Ramadan, da wa'adin farko na yarjejeniyar ke cika a ranar Asabar 1 ga watan Fabrairu 2025.

Karin bayani: EU ta bukaci dakatar da farmakin Isra'ila a yamma da kogin Jordan 

Gwamnatin Isra'ila ta sanar da cewa ta dauki wannan mataki ne domin bai wa jakadan da shugaba Donald Trump na Amurka ya nada kan al'amuran da suka shafi Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff, damar gabatar da sabbin matakai da shawarwari kan sulhun da kuma bai wa al'ummar musulmi a Gaza damar gudanar da ibada har ma da Yahudawa da za su gudanar da bikin Passover a watan Afrilu.

Karin bayani: Isra'ila da Hamas sun yi musayar fursunoni a karo na shida 

Mai magana da yawun Hamas Hazem Qassem ya fitar da sanarwar cewa kungiyar ba ta amince da bukatar tsawaita wa'adin farko na yarjejeniyar ba, abin da Hamas ta ke bukata shi ne aiwatar da daftarin farko kamar yadda dukkanin bangarorin biyu suka amince da hakan.

A yarjejeniyar da aka cimma a watan Janairu an bukaci dukkan bangarorin biyu dasu ajiye makamai har zuwa lokacin da za a kammala yarjejeniyar wanda kuma zai kawo karshen yakin da ake gwabzawa.

 


News Source:   DW (dw.com)