Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya gabatar da jawabin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatinsa da mayakan kungiyar Hezbollah na Lebanon. Firaminstan ya tabbatar da haka bayan kammala ganawa da jiga-jigan gwamnatinsa. Tun farko manyan jami'an gwamnatin Lebanon sun nuna fata kan samun amincewa da wannan yarjejeniyar tsagaita wutar.
Karin Bayani: Isra'ila ta kai wani sabon hari a tsakiyar birnin Beirut na Lebanon
Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da mayakan Hezbollah, a wannan Talata dakarun Isra'ila sun kai hare-hare ta sama birnin Beirut fadar gwamnatin Lebanon, wuraren da ake dauka tungar mayakan na Hezbollah da ke samun goyon bayan kasar Iran.