Wasu manyan shugabannin Hamas sun yi watsi da zargin da Isra'ila ke yi na cewa, kungiyar ta Falasdinawa ta na jan-kafa kan wasu batutuwan da ke kunshe a yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka sanar a wannan Laraba.
Wani jami'in Hamas Sami Abu Zuhri ya shaida wa kamfanin dilancin labaran Faransa na AFP cewa, ikirarin firayim ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu game da zargin bashi da tushe. Haka shi ma wani jami'in sashin siyasa na Hamas Izzat al-Rishq, ya jaddada cewar, a shirye kungiyar take wajen tabbatar da wannan yarjejeniyar da masu shiga tsakani suka sanar.
A wannan Alhamis din ce dai Isra'ila ta zargi Hamas da ja da baya kan wasu sassa na yarjejeniyar tsagaita wutar, da kuma batun sakin wadanda ake garkuwa da su a yakin Gaza, tare da kai sabbin hare-hare ta sama gabanin kuri'ar da majalisar ministocin kasar za ta kada.
Tuni dai ofishin firaminista Benjamin Netanyahu ya ce majalisar ministocin Isra'ila, wadda har yanzu ba ta amince da yarjejeniyar ba, ta jinkirta zamanta don kada kuri'a kamar yadda aka tsara, har sai masu shiga tsakani sun tabbatar da cewa Hamas ta amince da duk tanadin yarjejeniyar."