A wannan Asabar Majalisar ministocin Isra'ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Hamas, hukuncin da ya kawo karshen zaman zullumin da ake yi na yiwuwar fara aiwatar da yarjejeniyar a karshen wannan makon, sakamakon yadda ministoci masu tsattsaurar ra'ayi ke adawa da matakin. Wadanda ma'aikatar ta bayyana samun 'yancin nasu, ciki har da magidanta da mata da kuma yara kanana da ake sa ran a sake su kafin wayewar garin Lahadi.
Tun da fari ta fitar da jerin fursononin Falasdinawa 95 wanda yawancin mata ne da za a yi musayarsu da 'yan Isra'ila da ake tsare da su a Gaza. Kakakin ma'aikatar, Moga Katz ta ce, adadin fursononin da za a saki a musayar fursononi na farko zai danganta ne da yawan mutane da Hamas ta sake.