Isra'ila da Hamas sun yi musayar fursunoni a karo na shida a yau Asabar a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza wadda ta kusa wargajewa a makon nan, inda Isrla'ilawa uku da kuma Falasdinawa 369 suka shaki iskar 'yanci.
Hamas ta mika wa kungiyar agaji ta Red Cross mutanen uku da suka hadar da Sacha Trupanov mai shekaru 29 da Sagui Dekel-Chen mai shekaru 36 da kuma Yaïr Horn mai shekaru 46 a birnin Khan Younis da ke kudancin Gaza.
Karin bayani: Hamas ta amince da sakin Isra'ilawa 3 da ta yi garkuwa da su
Masu aiko da rahotanni sun ce ba bu alamun galabaita a jikin wadannan fursunoni dukanninsu 'yan Isra'ila da ke da tsatso da wasu kasashen bayan sun kwashe kwanaki kusan 500 ana garkuwa da su.
A daidai wannan lokaci motoci shake da fursunonin Falasdinu suka isa kudancin Gaza da kuma Gabar Yamma da Kogin Jorgan inda suka samu tarba daga dandazon jama'a da 'ya uwa da dangi.
Karin bayani:Trump ya bai wa Hamas wa'adin sakin Isra'ilawa da ke Gaza
Wannan zango na shiga na musayar fursunonin na zuwa a daidai lokaci da ake dakon zuwan sakataren harkokin wajen Amurka Mario Rubio wanda zai isa Isra'ila da maraicen yau.