Kasar Iran ta bayyana cewa tana duba bukatar da kasar Siriya ta gabatar mata na neman dakarun da za su taimaka wajen dakilke hare-haren 'yan tawaye da gwamnatin kasar take fuskanta. Abbas Araghchi ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya ce gwamnatin ta Siriya da ke dasawa da kasarsa ta bukaci tura mata dakaru, kuma yanzu haka ana duba wannan bukata.
Karin Bayani: Faransa ta bukaci kare rayukan fararen hula a Siriya
Haka ya biyo bayan yadda wasu 'yan tawaye masu kaifin kishin addinin Islama da ke yankin arewacin Siriya suka kwace garin Aleppo birnin na biyu mafi girma a kasar daga hannun dakarun gwamnatin Siriya. Tuni gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ta kasar ta Siriya ta nemi taimakon soja da makamai daga kasashen da suke kawance domin dakile abin da ta kira 'yan ta'adda da masu ba su taimako.