Iran ta yi gwajin tauraron dan adam

Iran ta yi gwajin tauraron dan adam
Karo na biyu kenan da kasar Iran ke harba tauraron dan adam zuwa sararin samaniya a binciken da Tehran ke yi kan gwajin fasahar sadarwa.

Iran ta harba wani tauraron dan adam a wannan lahadi na gwajin fasahar sadarwa wato satellite, wannan shi ne karo na biyu da take harba tauraron mai suna Zuljanah wato bayan wanda tayi a bara. 

Kasar na fatan ganin ta yi amfani da fasahar a fannoni sadarwa da suka hada da rediyo da talabijin da sauransu, baya ga iya amfani da shi a wasu gwaje-gwajen fasahohi na zamani. Mahukuntan na Tehran ba su fito sun yi karin bayani kan nasarar gwajin tauraron ko kuma akasin hakan ba kamar yadda ta saba fadi a baya.


News Source:   DW (dw.com)