Iran ta saki 'yar gwagwarmaya Narges Mohammadi daga kurkuku

A Larabar nan ce Iran ta saki 'yar gwagwarmayar nan Narges Mohammadi da ta taba lashe lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel daga kurkuku, domin zuwa a duba lafiyarta, kamar yadda mai gidanta Taqi Rahmani ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Karin bayani:Ana gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Iran

Daga cikin laifukan da suka sanya gwamnatin Iran daure Narges Mohammadi akwai yada farfagandar kin jinin gwamnatin, da sauran laifuka.

Karin bayani:Iran na azabatar da wata 'yar fafutuka

Wani sako da lauyanta mai suna Mostafa Nili ya wallafa a shafinsa na X a yau din nan, ya ce ofishin mai gabatar da kara na Iran ne ya sahale sakin nata na tsawon makonni uku, bayan karbar rahoton gwaje-gwajen da likitoci suka yi mata, da suka tabbatar da cewa hakika tabarbarewar lafiyarta ta yi kamarin da ya zama wajibi a bata kulawa ta musamman.


News Source:   DW (dw.com)