Hukumomi a Iran sun ce har yanzu ba su sauya manufarsu kan kera makaman nukiliya ba. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Nasser Kanani, ne ya shaida wa 'yan jarida hakan a wannan Laraba, inda ya ce mahukunta a Tehran na da fatwa da ta haramta kera makaman kare dangi.
Wannan bayani dai ya biyo bayan wata hira da gidan talabijin na Aljazeera ya yi da wani babban jami'in gwamnatin kasar, wanda ya ce Iran na da kayan aikin da za ta iya sarrafa makaman kare dangi.