Mijin Narges mazaunin birnin Paris,Taghi Rahmani, ya zargi hukumar gidan kurkukun mata na Qarchak da ke kusa da Tehran a kan shafukan sada zumunta da kwace maganin huhu da danginta suka aika mata. Narges, mai shekaru 50, wacce ke fama da cututtukan huhu da zuciya, an kwantar da ita a asibiti sakamakon bayyanar rashin numfashi da kuma ciwon zuciya, amma tun bayan da ta koma gidan yari an hanata samun wasu magungunan da take bukata a cewar Amnesty International. A halin yanzu, Narges Mohammadi tana zaman gidan yari na shekaru goma da watanni takwas a wasu kararraki guda biyu, ciki har da hukuncin daurin rai da rai a kan yada farfaganda nuna kiyaya ga gwamnatin Kasar Iran.