IOM ta ce akwai karin hadarin samun mace-mace a Sudan

Hukumar ta IOM dai na gargadin cewa jan kafa wajen taimaka wa Sudan na iya zama sanadin mutuwar dubban rayukan fararen hula cikin watanni masu zuwa.

Kawo i yanzu a cewar hukumar, kaso 21% ne na tallafin da kasashen duniya suka yi alkawari aka iya samarwa ga kasar kuma da ke cikin tsananayin yanayi na bukatar dauki.

Kasar Sudan da ke fama da yaki, na cikin hali na yunwa da cututtuka gami da ibtila'in ambaliya.

Sama da mutum miliyan 10 ne dai suka rasa gidajensu a Sudan, yayin da fiye da miliyan biyu suka bar kasar baki daya.


News Source:   DW (dw.com)