Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta sanar da karshen watan nan a matsayin lokacin da za ta kawo karshen aikin sabuntawa da karbar katin zaben da za a yi a shekara mai zuwa. Matakin ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke na ci gaba da rijistar masu jefa kuri’ar, inda kotun ta ce hukumar zaben na da ikon dakatar da aikin.
Tun da farko kungiyar SERAP mai faftukar kare 'yancin dan Adam ce dai ta shigar da karar domin dakatar da hukumar INEC rufe aikin rajistar masu zaben a karshen watan da ya gabata.