Firaministan Indiya Narendra Modi da takwaransa na Spain Pedro Sanchez, sun kaddamar da cibiyar kera jiragen sama na yaki mai zaman kanta ta farko a Delhi babban birnin Indiya, a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fadada ayyukanta na kere-keren kayan yaki.
Karin bayani:Indiya da Chaina za su yi sulhu kan iyakar da ke tsakaninsu
Shugabannin biyu sun kaddamar da bikin bude cibiyar a wani gagarumin taro da aka gudanar tare da nunin motocin yaki a jihar Gujrat, inda daruruwan mutane suka yi jerin gwano suna daga tutocin yabo.
Karin bayani:Spain ta ceto 'yan ci-rani 516 daga Afirka a tsibirin Canary
Ziyarar ta Mr Sanchez a Indiya ita ce ta farko da wani shugabanta ke yi a Indiya cikin shekaru 18, kuma zai gana da Mr Modi a Litinin din nan don tattauna batutuwan da suka shafi bunkasa harkokin kasuwanci da cinikayya a tsakanin kasashen biyu.